Sen Ndume Ya Roฦe Shugaba Tinubu Da ECOWAS Dasu Janye Takunkumin da suka Sanya wa ฦasar Nijar Musamman Ta Fuskar Tattalin Arziki.
Sanata Mohammed Ali Ndume ya bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da kungiyar raya tattalin arzikin ฦasashen yammacin Afirka ECOWAS dasu dage takunkumin da suka kakaba wa jamhuriyar Nijar ta fuskar tattalin arziki da kasuwanci da dai sauransu. A cewarsa, takunkumin na tsawon watanni biyar yana matukar shafar al'ummar Nijar, maimakon Gwamnatin mulkin soja ฦarฦashin Jagorancin Janar Abdourahamane Tchiani. Ndume ya yi wannan kiran ne a jiya, a gidan sa na Government Reserved Area (GRA), da ke Maiduguri, jihar Borno, a lokacin da ya koka kan takunkumin da aka kakaba wa mutane miliyan 26 na kasar da ke amfani da harshen Faransanci a Yammacin Afirka. Baya ga taษarษarewar tattalin arziki da ake fama da shi a Nijar, al’ummar yankunan kan iyakokin jihohin Kano, Zamfara, Borno, Katsina, Sokoto, Jigawa, Kebbi da Yobe, a Najeriya, su ma suna fama da matsalar tattalin arziki da kasuwanci. Ya ce ya kamata a sanya takunkumi kan Gwamnatin Tchiani da ta hambarar da Gwamnatin shugaban Mohame