A Najeriya wasu sun mayarda masallaci gidajen su, su shiga su zauna suyi ta cin mutumcin mutane suna zagin da ko a toilet din gidan su basa yi, amma za su shigo dakin Allah su yi. / Sheriff Almuhajir.

Masallaci ko da dukiyar ka ka gina shi ya zama dakin Allah ba na ka ba ne, amma a Najeriya wasu sun mayarda masallaci gidajen su, su shiga su zauna suyi ta cin mutumcin mutane suna zagin da ko a toilet din gidan su basa yi, amma za su shigo dakin Allah su yi.  

Tun suna zagin ma su addinai mabanbanta, su ka dawo zagin ma su sabanin akidah suka tsallake yan akidah daya suka shiga kungiya daya, suka dawo masallaci daya kai yanzu gar da gar ma suke kama sunan juna suna narka bakaken maganganu.

Sun mayar da mimbarin wajen yakar sabanin ra'ayi na siyasa ne ko na neman duniya, kwanannan wani malami a Kano yake amfani da majlisin karatu don tallar dan takara, kuma gar da gar yake zagin Gomna mai ci, kuma ya sani tsakani da Allah dukkan su da constitution za su yi mulki ba da al-Qur‘ani ba. Idan wanda ba sa so ya samu daukaka su shiga mimbari su ce ba sa so, idan yayi kuskure su kambama, idan ya yi alheri su kore.

Duk sun koyawa ya'yan ku rashin kunya da zagin manyan mutane, sun sa yayan ku sun dauka haka Annabi yayi ta cin mutumcin mutane wajen fadin gaskiya, saboda haka suke gani shine tafarki ingantacce. 

Kuma sun haddasa muguwar gaba da kiyayya a junan su, ta kai da za su samu dama su dauki makamai wata rana sassare juna za su yi su karkashe juna, kai da za'a ba su dokar hukunta mutane to tun suna kashe mabanbanta addini, za su dawo kashe ma su sabanin ra'ayi da su. Wai su dole sai an bi abunda suke yi, bayan gar da gar muna ganin abunda suke yi din ba haka Annabi SAW yayi ba, ba kuma ba haka yake so ba.

Ni dai shawara ta, ku kiyaye ya'yan ku ku san wajen wanda za ku kai su karatu, domin abun kara gaba yake yi.
Ga masu bukatar a tallata musu hajijinsu a mahajoji dabam-dabam zasu iya bibiyarmu ta wadanda gurare kamar haka .
Da kuma 

Comments

Popular posts from this blog

Daga Kamfanin A.S.U Media -- Sakon taya murnan samun Sarautan Wazirin katagum.

Sanata Halliru Dauda Jika ya sauya Sheka daga Jam'iyyar NNPP zuwa Jam'iyyar APC.

Dan Majalisan Tarayya,Ya rabawa Al'ummar Mazabar sa bututun magudanar: Masai.Hon Aminu Aliyu Gari