Sen Ndume Ya Roƙe Shugaba Tinubu Da ECOWAS Dasu Janye Takunkumin da suka Sanya wa ƙasar Nijar Musamman Ta Fuskar Tattalin Arziki.

Sanata Mohammed Ali Ndume ya bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da kungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka ECOWAS dasu dage takunkumin da suka kakaba wa jamhuriyar Nijar ta fuskar tattalin arziki da kasuwanci da dai sauransu.

A cewarsa, takunkumin na tsawon watanni biyar yana matukar shafar al'ummar Nijar, maimakon Gwamnatin mulkin soja Ƙarƙashin Jagorancin Janar Abdourahamane Tchiani.

Ndume ya yi wannan kiran ne a jiya, a gidan sa na Government Reserved Area (GRA), da ke Maiduguri, jihar Borno, a lokacin da ya koka kan takunkumin da aka kakaba wa mutane miliyan 26 na kasar da ke amfani da harshen Faransanci a Yammacin Afirka.

Baya ga taɓarɓarewar tattalin arziki da ake fama da shi a Nijar, al’ummar yankunan kan iyakokin jihohin Kano, Zamfara, Borno, Katsina, Sokoto, Jigawa, Kebbi da Yobe, a Najeriya, su ma suna fama da matsalar tattalin arziki da kasuwanci. Ya ce ya kamata a sanya takunkumi kan Gwamnatin Tchiani da ta hambarar da Gwamnatin shugaban Mohamed Bazoum ba bisa ka'ida ba a ranar 26 ga Yuli, 2023.

"Shawarar da ECOWAS ta yanke na sanyawa Nijar takunkumin tattalin arziki, ya kasance cikin Gaggawa, Maimakon Majalisar Dokoki ta tattauna da Gwamnatin mulkin soja," inji shi, Yana mai gargadin cewa kimanin 'yan Gudun hijira 100,000 daga ƙananan hukumomin Abadam, Guzamala da Mobbar ne ke fakewa. Lardin Diffa sama da Shekaru goma. Don haka Ndume ya yi kira ga Tinubu da ya tattauna da Tchiani ta hanyar tura tsaffin Shugabannin kasa na soja Guda hudu da suka hada da Janar Yakubu Gowon mai ritaya da Abubakar Abdulsalami da Muhammadu Buhari da Ibrahim Babangida.

Comments

Popular posts from this blog

Daga Kamfanin A.S.U Media -- Sakon taya murnan samun Sarautan Wazirin katagum.

Sanata Halliru Dauda Jika ya sauya Sheka daga Jam'iyyar NNPP zuwa Jam'iyyar APC.

Dan Majalisan Tarayya,Ya rabawa Al'ummar Mazabar sa bututun magudanar: Masai.Hon Aminu Aliyu Gari