Sanata Halliru Dauda Jika ya sauya Sheka daga Jam'iyyar NNPP zuwa Jam'iyyar APC.

Ajiya asabar 30-09-2023 Sanata Halliru Dauda Jika Dokajin Bauchi ya Ziyarci Jihar Bauchi Inda ya Fara yada zango a karamar Hukumar Ningi, Dan halartan Nadin Sarautan Ambassador Shu'aibu Ahmad amatsayin wazirin ningi.YouTube Channel
Bayan kammala Nadin Sarautan Sai ya wuce zuwa fadar Mai martaba Sarkin Ningi Dr Yunusa Muhammad Dan yaya, Dan gabatar wa Mai martaban gaisuwa irin ta Martabawa da Girmamawa GA Sarkin a matsayinsa na uban kasa .

Daga nan Sai ya Miki zuwa cikin kwaryar Jihar Bauchi Inda ya Fara ziyartar fadar Mai martaba Sarkin Bauchi, nanma duk Dan ya halarci Nadin sarautar Alh Yakubu Ibrahim lame Da ga Marigayi Dr Yakubu lame Inda aka nadashi amatsayin Santurakin Bauchi.

Daga nan Sai Dokajin ya ziyarci tsohon Sakataren Gwamnati na kasa a gidansa dake nan Jihar Bauchi Alh  Mahammad Yayalle Ahmed.

Har ila yau bai tsaya nanba, Sai ya Kara ziyartan Gidan Marigayi Dr Ibrahim lame Dan taya Yan'uwa, Iyaye da abokan arziki murnan tabbatar da Sarautan da Mai martaba yayi wa ahalin Gidan Marigayin.

Bayan fitowarsa daga Gidan Marigayi Dr lame Sai ya wuce Kai tsaye zuwa gidansa dake GRA anan cikin Garin Bauchi.

Bayan kammalawar sa da gidan nasa, Sai ya wuce zuwa Garin Kafin Madaki dake karamar Hukumar Ganjuwa, Inda ananne ya karbi tikitin Shedar Dawowar sa Jam'iyyar APC, daga matakin Gunduma kamar yanda kowani Dan Jam'iyya yake karba Dan tabbatuwarsa cikakken dan Jam'iyya.

Sanann ananne ya bada kyautar Mota guda daya wa Shugaban Jam'iyyar APC na karamar Hukumar Ganjuwa da kuma mashina guda Ashirin da Daya wa wasu daga cikin Excos din da suka tabbatar masa da mubaya'arsu agareshi, Inda kuji daga bakinsa ...l

Daga Karshen Jawabin nasa Dokajin ya karkarene da yi wa Jam'iyyar APC dama Al'ummar Jihar Bauchi baki Daya, addu'ar fatan Alkhairi tareda zamannlafiya cikin aminci da kwanciyar hankali.Ziyara tareda karbar katin sauyin sheka daga NNPP zuwa APC

A.S.U Media /
Dokaji-Tv

Comments

Popular posts from this blog

Daga Kamfanin A.S.U Media -- Sakon taya murnan samun Sarautan Wazirin katagum.

Dan Majalisan Tarayya,Ya rabawa Al'ummar Mazabar sa bututun magudanar: Masai.Hon Aminu Aliyu Gari