Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya yi kira da a yi gyara ga dokar zabe ta 2022
Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya yi kira da a yi gyara ga dokar zabe ta 2022.
Ya ce duk da cewa dokar zaben kasar za a iya cewa ita ce mafi inganci a tarihin Najeriya, amma ba ta cika ba; kuma akwai bukatar karin gyara.
Jega ya yi wannan jawabi ne a wani taron kwana biyu da Cibiyar Nazarin Majalisun Dokoki da Dimokuradiyya (NILDS) ta shirya wa Sanatoci a Ikot Ekpene, Jihar Akwa Ibom.
Gyare-gyaren, in ji shi, ya kamata su sanya watsar da sakamako ta hanyar na'urar Mai anfani da lantarki ta daga zabuka masu zuwa a shekarar 2027.
Ya kuma ce kamata ya yi ace ba shugaban kasa ne ke nada shugaba da kwamishinonin INEC na kasa ba domin kwato hukumar daga bangaranci.
Ya ce kamata ya yi a sake duba dokar domin tabbatar da cewa an warware duk wasu al’amura da suka taso daga gudanar da zabe tare da yanke hukunci kafin ranar da za a rantsar da su.
Comments
Post a Comment