Posts

Ku kwantar da hankulanku,Sanan Ku marawa wannan sabuwar Gwamnatin Baya, Cewar Hamshakin Dan Kasuwa Alh Abdulsamad Rabi'u Mamallakin Kamfanin BUA

Image
Ku kwantar da hankulanku, Sanan Ku marawa wannan sabuwar Gwamnatin Baya, Cewar Hamshakin Dan Kasuwa Alh Abdulsamad Rabi'u Mamallakin Kamfanin BUA Sannan ya jaddadar da saukake farashin simintin kafaninsa daga Naira Dubu biyar # 5,000 zuwa Naira dubu Uku da dari biyar # 3500. Inda wannan sabon farashin zai fara amfani daga ranar 31 GA watan December wannan Shekarar . A.S.U Media Sashin tallace-tallace na kamfanin A.S.U Media

Gwamna Dikko Radda Ya Fitar Da Sama Da N500m Don Biyan Tsaffin Ma'aikatan Jihar Katsina Giratuti Da Fansho.

Image
Gwamna Dikko Radda Ya Fitar Da Sama Da N500m Don Biyan Tsaffin Ma'aikatan Jihar Katsina Giratuti Da Fansho Majiyar mu ta ruwaito Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Radda ya amince da fitar da zunzurutun kudade har naira miliyan dari biyar da arba'in da uku, da dubu ɗari da goma, da dari bakwai da ashirin da kuma kwabo shida a matsayin kudaden da za a biya tsaffin ma'aikatan jihar Katsina na karshen shekarar 2019 Kamar yadda ruhoton ya tabbatar hakan na kunshe a sanarwar manema labaru wadda babban mai taimaka wa gwamnan a fanin yada labarai a kafafen sadarwar zamani Isah Miqdad ya fitar a yau  din Nan Litinin. "Mai Girma Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD ya amince da a fitar da kudi Naira 543,110,720.06 don a biya sauran kudaden ajiye aiki na 'gratuity' da fansho na karshen shekarar 2019." Inji Miqdad Shashin Tallace-tallace na kamfanin A.S.U Media

Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya yi kira da a yi gyara ga dokar zabe ta 2022

Image
Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya yi kira da a yi gyara ga dokar zabe ta 2022. Ya ce duk da cewa dokar zaben kasar za a iya cewa ita ce mafi inganci a tarihin Najeriya, amma ba ta cika ba; kuma akwai bukatar karin gyara. Jega ya yi wannan jawabi ne a wani taron kwana biyu da Cibiyar Nazarin Majalisun Dokoki da Dimokuradiyya (NILDS) ta shirya wa Sanatoci a Ikot Ekpene, Jihar Akwa Ibom. Gyare-gyaren, in ji shi, ya kamata su sanya watsar da sakamako ta hanyar na'urar Mai anfani da lantarki ta daga zabuka masu zuwa a shekarar 2027. Ya kuma ce kamata ya yi ace ba shugaban kasa ne ke  nada shugaba da kwamishinonin INEC na kasa ba domin kwato hukumar daga bangaranci. Ya ce kamata ya yi a sake duba dokar domin tabbatar da cewa an warware duk wasu al’amura da suka taso daga gudanar da zabe tare da yanke hukunci kafin ranar da za a rantsar da su. WhatsApp Channel A.S.U Media Facebook page A.S.U Media

Kotu ta bayyana ranar da zata yanke hukuncin Shari'ar dake gaban na zaben Shugaban kasa. Tareda bayyana sunayen Alkalai guda bakwai Wanda sune zasu yanke hukuncin .

Image
A yau kotu ta ayyana ranar Alhamis 26-10-20 Akan ranar da zata zantar da hukunci Kan karar da Atiku da Obi Shuka shigar gabanta. Kotunnan ta bayyana sunayen manyan Alkalen kasa guda bakwai Wanda sune zasu gabatar da hukuncin Shari'ar. 1 -Justice John Iyang Okoro 2 -Justice Uwani Musa Abba-Aji 3 - Justice Ibrahim Saulawa 4 - Justice Muhammed Lawan Garba 5 - Justice Tijjani Abubakar 6 - Justice Adamu Jauro 7 - Justice Emanuel Agim Wadannan alkalan da zasu dale karagar Kujeran yanke hukuncin Shari'ar dake gaban kotun , Wanda Atiku Abubakar da Peter Obi Suaka shigar a gaban Kotun.

kotu ta Fara sauraran Shari'ar Major- General Alkali Wanda aka masa kisan gilla a Jos a shekaru baya

Image
Sai yau aka fara sauraran shari'ar kisan gillar da aka yi wa Manjo-Janar Alkali a Jos. An gurfanar da mutane 21 da ake zargin da kisan marigayin a kauyen Guchwet da ke Plateau. Marigayin ya rasa ransa ne a kan hanyarsa ta zuwa Bauchi daga birnin Abuja a shekarar 2018.

Kotun ɗaukaka kara ta tabbatar da zaben Tambuwal a matsayin Sanatan Sokoto ta Kudu.Cikakken Rahoton Zai Zo Daga Baya

Image
Kotun ɗaukaka kara ta tabbatar da zaben Tambuwal a matsayin Sanatan Sokoto ta Kudu. Zaku iya bibiyar A.S.U Media a Sauran shafinkanmu a Manhajojin Facebook, Twitter, Instagram YouTube, WhatsApp Channel dinmu a wannan link din dake kasa. A.S.U Media Facebook page A.S.U Media YouTube Channel  https://www.youtube.com/@a.s.umedia8014 A.S.U Media WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VaA2BdxGZNCky49CCX3Q  https://asumediablog.blogspot.com/?m=1 A.S.U Website A.S.U TIKTOK tiktok.com/@a.s.u.media A.U.S Tiktok INSTAGRAM :- https://instagram.com/a.s.u_media?igshid=MzNlNGNkZWQ4Mg==

Dan Ganduje Ya ziyarci Dr Rabi'u Kwankwaso a gidansa dake Bunpai a kano

Image
YANZU - YANZU: Babban ɗan gidan Ganduje wanda dama shi ɗan Kwankwasiyya ne Abdul’aziz Abdullahi Umar Ganduje, ya ziyarci jagoran kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a gidansa dake Bompai Kano.