Najeriya ba ta uzirin dawwama cikin fatara da talauci -Shettima

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim, ya bayyana cewa Najeriya ba ta da wani uzirin da za ta ci gaba da dawwama cikin ƙangin talauci, ƙuncin rayuwa da fatara.

Ya yi wannan bayani a lokacin da ya ke rantsar da Kwamitin Inganta Abinci Mai Gina Jiki, ranar Juma’a, a Abuja.

Kafa kwamitin ya bijiro ne saboda ƙoƙarin da Gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ke yi na magance matsalar rashin abinci mai gina jiki.


Kwamitin zai jagoranci aikin yaƙi da yunwa da rashin abinci mai gina jiki a faɗin Najeriya.

Da ya ke jawabi wajen ƙaddamar da Kwamitin Samar da Abinci Mai Gina Jiki (NCWC), Shettima ya jaddada muhimmancin haɗa kai da Kwamitin Inganta Abinci da Kula da Abinci Mai Gina Jiki na Ƙasa (NCFN).


Yayin da Shettima ya kai ziyara a ƙauyen Tudun Biri, inda Sojoji suka jefa bam bisa kuskure kan masu Maulidi, hankalin Mataimakin Shugaban Ƙasa ɗin ya tashi da ya ga yara ƙanana marasa galihun abinci mai gina jiki a jikin su.

Dangane da haka ne ya ce, “Ba mu da wani uzirin da Najeriya za ta ci gaba da dawwama a cikin talauci da fatara.”

Ya ce Allah ya albarkaci ƙasar nan sosai da albarkatun ƙasa. Don haka bai kamata fatara, talauci da rashin abinci mai gina jiki su na yi wa Najeriya barazana ba.

Makonni uku da suka gabata, shi ma Shugaban Bankin Bunƙasa Ƙasashen Afrika, Akinwumi Adesina, ya jaddada cewa babu wani uzirin da Najeriya da Afrika za ta dawwama cikin ƙangin fatara da talauci

An bayyana cewa Afrika, nahiya mai aƙalla ƙarfin arzikin albarkatun ƙasa har dala tiriliyan 6.2, nahiya mai kashi 65 bisa 100 na ƙasar noma a faɗin duniya tare da ɗimbin matasa majiya ƙarfi, to babu wani dalili ko uziri da za’a bayar a ce irin wannan nahiya ta dawwama cikin ƙangin talauci da fatara.

Shugaban Bankin Bunƙasa Ƙasashen Afrika, Akinwumi Adesina ne ya yi wannan furucin a ranar Talata.

Ya ce tilas Afirka ta tsaya ta yi wa kan ta karatun ta-natsu, ta nemo hanyoyin da za ta magance matsaloli da ƙalubalen da ‘yan nahiyar ke fuskanta.

Akinwumi ya ce a cikin nahiyar dukkan hanyoyin magance waɗannan matsaloli su ke, ba a waje can ƙasashen Turai, Amurka da Asiya ba.

Ya yi wannan kira a Legas, yayin da ya ke gabatar da lacca, a taron cikar jaridar The Guardian shekaru 40 da kafawa.

An gudanar da laccar mai taken Yadda Afrika Za Ta Yi Bunƙasar da Duniya Za Ta Yi Shakkar Ta.

Adesina, wanda shi ne Gwarzon Jaridar The Guardian na 2021, ya ce a gaskiya bai kamata a ce Afrika ta na matsayin da ta ke yanzu a duniya ba.

Kan haka ne ya yi kira manyan ƙasashe masu arziki na cikin nahiyar cewa su miƙe tsaye su ƙarfafa gwamnatin su, a riƙa shugabanci tsakani da Allah, kuma a riƙa kula da arzikin ƙasa, maimakon almubazzaranci da wawurar dukiya da suka yi ƙaurin suna a Gwamnatocin ƙasashen Afirka.

“Wato idan muka alkinta albarkatun ƙasa bil haƙƙi da gaskiya a Afrika, to Afrika ba ta wani uzirin da zai sa ta dawwama cikin fatara da talauci.”

Comments

Popular posts from this blog

Daga Kamfanin A.S.U Media -- Sakon taya murnan samun Sarautan Wazirin katagum.

Sanata Halliru Dauda Jika ya sauya Sheka daga Jam'iyyar NNPP zuwa Jam'iyyar APC.

Dan Majalisan Tarayya,Ya rabawa Al'ummar Mazabar sa bututun magudanar: Masai.Hon Aminu Aliyu Gari